Connect with us

Labarai

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Published

on

Daga Bello Wakili, Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 18 da aka gudanar a birnin New Delhi na ƙasar Indiya.

A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya halarci manyan zaman taron tare da gudanar da ganawar ƙasa da ƙasa, da nufin inganta muradun Najeriya na tattalin arziki da diflomasiyya.

Ɗaya daga cikin muhimman ganawarsa ita ce da Firaministan Indiya, Narendra Modi, inda bangarorin biyu suka tattauna kan farfaɗo da cinikin ɗanyen man fetur da zuba jari da harkar magunguna da tsaro da fasahar zamani da harkar kuɗi ta zamani, makamashi mai sabuntawa da sauran muhimman fannoni.

Sanata Shettima ya kuma gana da Darakta-Janar na Ƙungiyar Ciniki ta Duniya, WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, inda ya sake tabbatar da goyon bayan Najeriya ga tsarin haɗin gwiwar ƙasashe da kuma samar da tsarin tattalin arzikin duniya mai bai wa kowa dama.

A wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isar da saƙon Shugaba Tinubu na yin garambawul ga tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin kuɗi na ƙasa da ƙasa, tare da gabatar da Najeriya a matsayin ƙofa zuwa babbar kasuwar Afirka da ke haɓaka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci ta nahiyar Afirka.

Najeriya ta kuma yi amfani da taron wajen ƙara ƙarfafa hulɗarta da ƙasashen BRICS mambobi da abokan hulɗarsu a fannoni da suka haɗa da noma, basirar wucin gadi, ababen more rayuwa na zamani, masana’antu, kiwon lafiya, makamashi da bunƙasa jarin ɗan Adam.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara