Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa, NAHCON, domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin nasara.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Aminu Usman, ya bayyana haka lokacin da ya karɓi tawagar NAHCON da ta kai ziyarar ban-girma Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce gwamnati na ci gaba da ba da muhimmanci ga jin daɗin mahajjata, yana mai cewa ƙoƙarin jihar wajen gudanar da aikin Hajji ya sanya ta kasance cikin jihohin da ke kan gaba a ƙasa.
Injiniya Aminu Usman ya tabbatar wa tawagar cewa jihar za ta ci gaba da riƙe wannan matsayi, tare da yabawa NAHCON bisa ƙoƙarinta na inganta ayyukan Hajji.

Tun da farko, Kwamishinan NAHCON mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Sheikh Muhammad Bin Uthman, ya bayyana wasu sabbin manufofin hukumar, ciki har da wajabcin duba lafiyar maniyyata aikin Hajji.
Ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi da NAHCON, domin tabbatar da ingantaccen tsari da nasarar aikin Hajji.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa tawagar ta ziyarci Jihar Jigawa ne domin tantance matakin shirye-shiryen jihar na aikin Hajjin 2027.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Mahajjata ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya karɓi tawagar, tare da zagayawa da ita wuraren da jihar ke amfani da su wajen gudanar da aikin Hajji.

Alhaji Labbo ya ce jihar a shirye take tsaf don aikin Hajjin 2027, inda ya ƙara da cewa an sayar da dukkan kujerun Hajjin da aka ware wa jihar ga maniyyata. Yana mai cewa, jihar ta nemi ƙarin kujeru a hukumance domin biyan buƙatar da ke ƙaruwa daga masu niyyar zuwa aikin Hajji.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
