Connect with us

Labarai

Bayan Sauya Sheƙa: Gwamna Yusuf Ya Amince da Kafa Majalisar Dattawan Kano

Published

on

Daga Abdullahi Jalaluddeen

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa  APC,  inda ya jagoranci gagarumar sauya sheƙa a siyasar Jihar Kano.

Sauya sheƙar ta haɗa da mambobi 34 na Majalisar Dokokin Jihar, dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44, da kuma daukacin masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani babban biki da aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnatn Kano.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Yusuf ya ce matakin sauya sheƙar ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da kuma tantance halin da jihar ke ciki a yanzu da burin da take da shi a gaba.

Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin yin aiki tare da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da nufin hanzarta ci gaban Kano tare da kawo ainihin amfanin dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar.

“Bayan shawarwari masu zurfi kan makomar Jihar Kano, ni tare da mambobi 34 na Majalisar Dokoki, dukkan ƙananan hukumomi 44 da kuma dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa, mun yanke shawarar shiga jam’iyyar APC domin yin aiki da shugabanci mai hangen nesa na Bola Ahmed Tinubu,” in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya ce Ajandar sabunta kudurori ta Renewed Hope ta Shugaban Ƙasa ta fara haifar da sakamako mai kyau a faɗin ƙasar, yana mai jaddada cewa Kano ba za ta iya zama a gefe ba a lokacin da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya zai buɗe ƙarin damammaki ga al’ummarta.

Ya ƙara da cewa rikice-rikicen siyasa da faɗa ba su taimaka wa kyakkyawan shugabanci, yana mai bayyana shugabanci a matsayin hidima ga jama’a ba gasa ba.

Gwamnan ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan mataki bai rage ƙoƙari da gudummawar dukkan waɗanda suka tsaya tare da shi a tafiyarsa ta siyasa ba.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su duba sauya sheƙar cikin adalci, yana mai jaddada cewa an ɗauki matakin ne da kyakkyawar niyya domin samar da ƙarin dama, musamman ga matasan jihar.

Haka kuma, Gwamna Yusuf ya sanar da amincewa da kafa Majalisar Dattawan Kano. Ya ce majalisar ba za ta kasance ta siyasa ba, kuma za ta zama cibiyar ba da shawara ga gwamnati domin inganta zaman lafiya, haɗin kai da kyakkyawan shugabanci a jihar.

A cewarsa, haɗin kai da Gwamnatin Tarayya zai taimaka wajen samar da yanayin siyasa mai tsafta da haɗin kai, tare da tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali na dogon lokaci.

 

“Muna buɗe sabon shafi bisa ginshiƙin haɗin kai, kwanciyar hankali da shigar kowa. Ƙofofinmu a buɗe suke ga dukkan al’ummar Kano,” in ji gwamnan, yayin da ya yaba wa shugabancin APC bisa goyon baya da halartar bikin sauya sheƙar.

Manyan shugabannin APC da dama sun halarci taron, ciki har da tsohon Shugaban APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Karamin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane, Abdullahi Ata Fagge; Sanata Kawu Sumaila; Shugaban APC na Jihar Kano; da kuma dukkan shugabannin ƙananan hukumomi 44, tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

 

 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara