Labarai
Sudan ta Kudu ta Bai wa Fararen Hula Umarnin Barin Yankunan da ke Hannun ‘Yan Adawa
Rundunar Sojin Sudan ta Kudu ta bai wa fararen hula da ƙungiyoyin agaji da ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya wa’adin sa’o’i 48 su bar yankunan da ke ƙarƙashin ikon ‘ƴan adawa a jihar Jonglei da ke gabashin ƙasar, gabanin fara wani babban farmakin soji.
Wannan umarni na zuwa ne kwanaki biyu bayan da babban hafsan sojin ƙasar ya shaida wa dakarunsa cewa suna da kwanaki bakwai su “murƙushe tawaye” a gabashin ƙasar, wanda hukumomi suka ce na iya zama barazana ga babban birnin ƙasar, Juba.
A cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudu SSPDF, Manjo Janar Lul Ruai Koang ya ce dole ne mutanen da ke zaune a yankunan da ke hannun ƙungiyar ƴan adawa ta Sudan wato SPLA-IO, su fice cikin wa’adin da aka bayar.
Ya ƙara da cewa dole ne kuma fararen hula su koma yankunan da ke ƙarƙashin ikon gwamnati domin tsaron lafiyarsu, yayin da sojoji ke shirin ƙaddamar da farmakin da suka sanya wa suna da “Dorewar Zaman Lafiya”.
Kakakin ya kuma yi gargaɗin cewa duk fararen hula masu ɗauke da makamai su miƙa su ga sojojin gwamnati, yana mai cewa duk wanda aka samu kusa da barikin ƴan adawa SPLA-IO za a ɗauke shi a ɗaya daga cikinsu a haɗa da shi a farmakin.
Ƙungiyar ƴan adawa SPLA-IO ba ta ce komai ba dangane da wannan Umurnin.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
