Labarai
Sudan Ta fitar da Gargadin Ambaliyar Ruwa a Jahohi 5
Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito.
Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan.
Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile.
Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa.
Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a Nilu sakamakon kuskuren ɗan adam ne da ya shafi babban dam na Ethiopia.
Sharaky ya ce injinan da ke kula da tafiyar da ruwan dam huɗu sun gaza aiki, wanda ya sa Ethiopia ta kasa shawo kan ruwan da kuma tura ruwan da ya wuce gona da iri zuwa Sudan.
Ethiopia a jiya ta ƙaryata zargin, inda ta ce dam ɗin ya taka muhimmiyar rawa wajen rage illar ambaliyar.
A kowacce shekara, matakin ruwa a Kogin Nilu yana ƙaruwa a watan Agusta saboda ruwan sama mai yawa a tsaunukan Ethiopia.
BBC/Hausa
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
