Labarai
Ebola: NOA Ta Shirya Gangamin Wayar da Kai a Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Yayin da ake samun ƙaruwar bullar cutar Ebola a wasu sassan duniya, Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) reshen Jihar Jigawa ta ce tana aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa, musamman Cibiyar Gudanar da Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a, domin wayar da kan al’umma kan matakan kariya daga wannan cuta mai haɗari.
Daraktan hukumar a jihar, Alhaji Ahmad Ibrahim, ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa ofishin Masanin Cututtuka Masu Yaduwa na Jihar Jigawa da ke Dutse.

Ya ce duk da cewa Najeriya ba ta samu rahoton bullar cutar Ebola ba, akwai buƙatar ɗaukar matakan kariya tun da wuri domin dakile ɓarkewar cutar.
Alhaji Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa hukumar na shirin gudanar da gangamin wayar da kai a faɗin jihar, wanda zai mayar da hankali kan kasuwanni, tashoshin mota, cibiyoyin kiwon lafiya, makarantu da sauran wuraren taruwar jama’a.
Ya ƙara da cewa za a kuma haɗa sarakunan gargajiya da shugabannin addinai cikin wannan shiri na wayar da kai domin tabbatar da nasararsa.
Da yake mayar da martani, Masanin Cututtuka Masu Yaduwa na Jihar Jigawa, Malam Isma’ila Mamuda, wanda ya karɓi tawagar NOA, ya tabbatar da cewa zuwa ranar 3 ga watan Yunin 2026, ba a samu ko da mutum guda ba da ke dauke da cutar Ebola a Najeriya.
Sai dai Isma’ila Mamuda ya bayyana cewa cibiyar ta samu umarnin fara aiwatar da matakan kariya da magunguna, waɗanda suka haɗa da wayar da kai da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma, sakamakon ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a wasu sassan duniya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
