Connect with us

Labarai

Hajjin 2026: Jigawa ta Fara Tantance Lafiyar Maniyyata

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa  maniyyata masu cikakkiyar lafiya ne kadai za a lamincewa zuwa aikin Hajjin 2026.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a Babban Asibitin Gwamnati na Hadejia yayin ƙaddamar da shirin tantance lafiyar maniyyata aikin Hajjin 2026 a hukumance.

Ya ƙara da cewa shirin na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi domin tabbatar da lafiyar  Alhazan jihar.

Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada cewa hukumar ta jajirce wajen bin ƙa’idojin Saudiyya, waɗanda suka tanadi cewa mutanen da ke da cikakkiyar lafiya ne kaɗai za su gudanar da aikin Hajjin.

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da tantancewar cikin adalci da gaskiya domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Wasu daga cikin maniyyatan sun yabawa hukumar bisa  yadda take gudanar da shirin.

Rediyon Nijeriya ya ruwaito cewa Darakta Janar ɗin ya samu rakiyar Daraktan Ayyuka, Alhaji Muhammad Garba.

 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara