Connect with us

Ilimi

Kungiyar Malamai ta Kasa ta Karrama Farfesa Abubakar Birnin Kudu

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Kungiyar Malamai ta kasa NUT ta karrama Babban Malamin addinin musulunci Farfesa Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu dangane da gudummawar da yake bayarwa ga harkar ilimi.

A jawabinsa, Shugaban kungiyar NUT reshen Karamar Hukumar Birnin Kudu, Alhaji Musa Muhammad, yace an shirya taron ne domin kara kwarin gwiwa ga wadanda ke bada gudummawa ga harkokin ilimi.

Yace kungiyar ta yi fafutukar bada karatun digiri a karkashin cibiyar aikin malanta ta kasa wato NTI da kuma karatun NCE a karkashin kwalejin ilimi da ke garin Gumel.

Da yake jawabi, Hakimin Birnin Kudu Alhaji Husaini Hassan Jibrin ya yi kira ga kungiyar NUT ta tabbatar da sa ido wajen ganin cewar dalibai na shiga aji domin koyon karatu kamar yadda yakamata.

Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Dr Builder Muhammad Uba wanda kansilan ayyuka Alhaji Haladu Maigari ya wakilta, ya jaddada goyon bayansa wajen kawo ci gaban ilimi.

Dr Builder Muhammad Uba ya yi kira ga daidaikun jama’a da kungiyoyi da su hada kai da karamar hukumar wajen tallafawa bangaren ilimi.

Da ya ke jawabi a madadin wadanda aka karrama, Farfesa Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu ya bayyana malami a matsayin ginshikin rayuwar kowace al’umma.

Ya kuma bayyana fatan dawo da tsarin nan da hakimai ke jagorantar shigar da yara makaranta a can baya.

An karrama wasu mutane da kungiyoyi 14 bisa gudummawar da su ke bayarwa ga ci gaban ilimi a yankin.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, daga cikin wadanda kungiyar ta karrama sun hada da tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji Injiniya Magaji Da’u Aliyu da tsoffin shugabannin karamar hukumar, Alhaji Khalid Ibrahim da Alhaji Magaji Yusuf Gigo.

Sai Shugaba Mai ci yanzu na karamar Dr. Builder Muhammad Uba da tsohon Dan Majalisa Injiniya Sirajo Muhammad da tsohuwar babban sakatariya, Hajia Uwani Jafaru da Hajia Umma Abdulkadir Fanini da gidauniyar marayu da Alyateem da gidauniyar Baraya.

Taron ya samu halartar Dagacin Babaldu, Alhaji Usman Lamido wanda ya wakilci tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Dr. Sule Lamido da Babban Sakatare Alhaji Umar Isa da dai sauran jama’a.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara