Ilimi
Wata Gidauniya Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mata A Nasarawa
Gidauniyar fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar.
Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin taron horarwa na kwanaki uku da aka shirya ga masu ruwa da tsaki kan batun mata, zaman lafiya da tsaro, wanda gidauniyar ta shirya.
Mista Maduoma, wanda Jami’in Shari’a da Albarkatun Ƙasa na Gidauniyar, Mista Ifeyinwa Akwiwu, ya wakilta, ya ce shirin wani ɓangare ne na aikin gidauniyar mai taken “Ƙarfafa tsarin adalci ta hanyar kare haƙƙin ɗan adam da bunƙasa zaman lafiya a Najeriya.”
Ya bayyana cewa ana aiwatar da wannan shiri ne a jihohi biyar — wato Benue, Nasarawa, Plateau, Kaduna da Imo, domin haɓaka ingantaccen tsarin haɗin kai da amfani da bayanai wajen magance rikice-rikice ta hanyar tsarin da ya dace da bukatun mata.
Ya ƙara da cewa gidauniyar, tsawon shekaru 27, tana aiki wajen inganta tsaron jama’a, zaman lafiya da adalci a Najeriya da ma nahiyar Afrika ta hanyar bincike da fadarwa akan dokoki, da haɗin gwiwa da gwamnati da ƙungiyoyin farar hula.
A nasa jawabin, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Nasarawa, Barista Isaac Danladi, ya yaba da muhimmiyar rawar da mata ke takawa a al’umma, yana mai cewa ma’aikatarsa ta tanadi matakai na tabbatar da gurfanar da masu aikata ta’addancin fyade da cin zarafi ga mata, domin zama izina ga wasu.
Ita ma Kwamishinar Mata da Harkokin Jin Kai ta Jihar Nasarawa, Hajiya Hauwa Jugbo, ta bayyana shirinta na yin haɗin gwiwa da duk ƙungiyoyin da ke da sha’awar kare haƙƙin mata, tare da bada tabbacin cewa ma’aikatarta za ta goyi bayan cikakken aiwatar da dokoki da ke tabbatar da haƙƙin mata da adalci ga waɗanda aka zalunta.
Aliyu Muraki, Lafia.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
