Connect with us

Labarai

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnati Ta Tsara Hanya Mai Ma’ana Wajen Tafiyar Kasafin Kudi

Published

on

Majalisar Dattawa ta bukaci tawagar tattalin arzikin gwamnati da ta tsara hanya mai ma’ana domin komawa tsarin kasafin kuɗi da ya fi mayar da hankali kan fifikon aiki da sakamako, maimakon tsarin da ake amfani da shi a yanzu na “envelope system”.

 

Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Sani Musa, ne ya yi wannan kira a jawabin sa yayin wata ganawa ta musayar ra’ayi da tawagar tattalin arzikin gwamnati karkashin jagorancin Ministan Kudi, Mista Wale Edun.

 

Sanata Sani Musa ya ce kasafin kuɗi tsari ne na hasashe, don haka idan ba a cimma burin kudaden shiga ba, ba zai yiwu aiwatar da shi ya tafi daidai da abin da ake tsammanin samu ba.

 

Ya kara da cewa tsarin da ake bi a yanzu ba shi da inganci yadda ya kamata, domin ana sakin kashi 100 cikin 100 na kudaden overhead da na maimaituwa (recurrent), yayin da bangaren ayyukan ci gaba (capital projects) ke samun sifili.

 

Ya ce wannan ba abin yarda ba ne, kuma babbar matsala ce da ya kamata a duba.

 

A cewarsa, “Muna ganin jami’an gwamnati na yin tafiye-tafiye cikin sauki, ana cika biyan kudaden overhead da recurrent, amma kudaden ayyukan ci gaban da aka ware domin ‘yan Najeriya na nan a sifili. Wannan ba abin karɓa ba ne ga kwamitin.

 

Najeriya ba za ta iya ci gaba da yin kananan gyare-gyare ba yayin da ake bukatar garambawul na tsari baki daya.”

 

Sai dai kwamitin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta koma tsohon tsarin biyan ‘yan kwangila, maimakon sabon tsarin da aka mayar da shi tsakiya (centralized system), wanda ya jefa gwamnati cikin basussuka ga ‘yan kwangila da dama, har ma kan ayyukan da aka kammala a shekarar 2024, balle ma na 2025.

 

A nasu bangaren, mambobin kwamitin sun goyi bayan shugaban kwamitin tare da shawartar tawagar tattalin arzikin da ta inganta tsare-tsare da aiwatar da kasafin kuɗi, tare da gaggauta biyan ‘yan kwangila.

Haka kuma, a martanin da tawagar tattalin arzikin ta bayar, ta tabbatar wa kwamitin da ‘yan Najeriya cewa hasashen shekarar 2026 yana da kyau matuka dangane da aiwatar da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 58.472 da aka gabatar.

 

Ministan Kudi, Wale Edun, ya bayyana wa kwamitin cewa bashin Naira tiriliyan 152 da kasar ke da shi a halin yanzu ba duka daga rance kai tsaye aka tara shi ba. Ya ce kimanin Naira tiriliyan 30 sun fito ne daga bashin Ways and Means da wannan gwamnati ta gada, yayin da Naira tiriliyan 9 suka taso sakamakon sauyin canjin kudi (exchange rate adjustment).

 

Ya ce: “A halin yanzu, bashin gwamnati a Naira ya kai tiriliyan 152. Kimanin tiriliyan 30 sun fito daga Ways and Means da muka gada, sannan tiriliyan 9 sun taso daga gyaran canjin kudi. Saboda haka kusan rabin bashin gyare-gyare ne kawai, ba sabon rance ba ne. Sabbin rance tun daga 2023 suna cikin zangon tiriliyan 20.”

 

Tun da farko a farkon zaman ganawar da tawagar tattalin arzikin, kwamitin ya yanke shawarar rubuta wa Shugaba Bola Tinubu domin neman ya sauke Registrar-General na Hukumar Corporate Affairs Commission bisa zargin kin amsa gayyatar kwamitin akai-akai.

 

An cimma wadannan matsayai ne yayin zaman tattaunawar da tawagar tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Mista Wale Edun, tare da Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Sanata Atiku Bagudu; Akanta Janar na Tarayya, Dakta Shamseldeen Babatunde Ogunjimi; da Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (NRC), Zacch Adedeji.

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara