Connect with us

Labarai

An Raba Takin Zamani Da Kayan Noma Ga Manoman Jihar Zamfara

Published

on

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a kakar noman rani a faɗin jihar.

An ƙaddamar da shirin ne a ranar Alhamis a cibiyar Fadama III da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Noma ta jihar a Gusau.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, kayayyakin da aka raba suna da matuƙar muhimmanci wajen ƙara yawan amfanin gona, rage asarar da ake yi bayan girbi, da kuma bunƙasa noma mai ɗorewa.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan takin NPK 3,920, buhunan takin Urea 1,956, litar maganin kashe ciyawa 3,920, litar maganin kashe ƙwari 1,956, da kuma fakitin maganin shafa iri 3,920.

An tsara rabon ne domin kaiwa ga manoma a sassa daban-daban na jihar, musamman ƙananan manoma da ke dogaro da noma a matsayin hanyar samun abinci da kuɗin shiga.

A jawabinsa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa shirin na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin ƙara yawan noma, inganta tsaron abinci da kuma bunƙasa rayuwar al’umma.

Ya ce noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jihar, don haka wajibi ne gwamnati ta samar wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu su yi noma cikin inganci.

Ya bayyana cewa shirye-shiryen NG-CARES sun samar da tubalin da ya bai wa gwamnatin jihar damar cimma nasarori a bangaren noma, musamman ta hanyar tallafa wa dubban ƙananan manoma da iri masu inganci, magungunan gona da shawarwarin dabarun noma.

Gwamnan ya yi kira ga manoman Zamfara da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata, domin cimma manufar bunƙasa noma mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da irin waɗannan shirye-shirye wajen ƙara samar da abinci a cikin gida da rage dogaro da shigo da kayayyakin abinci daga ƙasashen waje.

Dangane da matsalolin tsaro, Gwamna Lawal ya amince cewa ƙalubalen tsaro na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar noma a halin yanzu. Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaro a yankunan karkara domin manoma su samu damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.

Haka kuma, ya yaba da goyon bayan da Gwamnatin Tarayya da abokan hulɗa na ci gaba ke bayarwa wajen aiwatar da shirin NG-CARES, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin bangarori ne kaɗai zai tabbatar da nasarar manufofin ci gaban noma da tattalin arziki a jihar.

Aminu Dalhatu/Gusau

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara