Labarai
Gwamnan Kano Ya Bada Ayukkan Kilomita 70 A Yankun Karkara 10
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa da suka dace a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da aikin samar da tituna masu tsawon kilomita 70 a tsakanin al’ummomin karkara 10 a kananan hukumomin jihar guda uku, wanda ya gudana a Rijiyar Gwangwan da Mil Goma a karamar hukumar Dawakin Kudu, wanda ya kai kilomita kusan 15 aka za a gudanar a wurare biyu na Karamar hukumar.
Ya ce aikin, wanda aka gudanar da shi tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Asusun Rayuwa Na (LLF), na da nufin inganta hanyoyin shiga yankunan karkara da yankunan da ke kusa da birane.
Gwamnan ya ce aikin ya kai sama da Naira miliyan dubu 11, inda aka ware Naira Miliyan dubu 2.6 don titin Mil Goma zuwa Yankatsari mai tsawon kilomita 7.2 da kuma hanyoyin Rijiyar Gwangwan mai tsawon kilomita 7.5.
Ya bukaci al’ummomin da suka amfana da su yi amfani da hanyar yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa duk wanda aka samu yana lalata kayayyakin bayan an kammala za a yi maganinsa da gaske.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da ayyukan raya ababen more rayuwa masu canza rayuwa a yankunan karkara.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
