Labarai
Gwamna Kefas Ya Zargi Jami’an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Haƙar Ba Bisa Ka’ida Ba
Daga Sani Sulaiman, Jalingo
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya zargi wasu jami’an gwamnati da hannu wajen taimaka wa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a sassa daban-daban na jihar, inda ya sha alwashin tsaftace harkar ta hanyar samar da sabon tsarin haƙar ma’adinai cikin gaskiya da bin ƙa’ida.
Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa da masu haƙar ma’adinai da ƙanana da matsakaita, wanda aka gudanar a Banquet Hall na TY Danjuma House da ke Jalingo.
Taron mai taken “Ayyukan Haƙar Ma’adinai Ƙanana da Matsakaita, Tasirinsu Ga Muhalli da Al’ummomin Masu Haƙar Ma’adinai, da Hanyar Samun Ci Gaba Mai ɗorewa a Jihar Taraba”, ya samu halartar jami’an gwamnati da ƙungiyoyin masu haƙar ma’adinai da wakilan al’ummomin da ake gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai.
Gwamnan ya ce ayyukan haƙar ma’adinai na ƙanana da matsakaita na dogaro da rayuwar dubban iyalai a Taraba, don haka ba za a iya haramta su gaba ɗaya ba, sai dai akwai buƙatar tsara su yadda za a tabbatar da tsaro, bin doka da kuma kare muhalli.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta samar da “Taraba Responsible Artisanal Mining and Community Health Standards”, wato ƙa’idojin da za su taimaka wajen kare hanyoyin samun ruwan sha da horar da masu haƙar ma’adinai da ma’aikatan lafiya, tare da samar da ingantaccen tsarin bayar da rahoton ayyukan da ka iya zama haɗari.
Kefas ya buƙaci shugabannin ƙungiyoyin masu haƙar ma’adinai da su tallafa wa gwamnati wajen wayar da kan mambobinsu game da manufofi masu aiki da sauƙin aiwatarwa, yayin da ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara lamuntar jami’an da ke taimaka wa ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Kula da Ma’adinan Ƙasa, Mista Matsai David Angye, ya bayyana taron a matsayin wanda ya zo a kan lokaci, yana mai cewa manufar gwamnati ba ita ce hana masu haƙar ma’adinai ƙanana da matsakaita samun abin dogaro da kai ba, sai dai horar da su da kuma ƙarfafa musu gwiwa domin gudanar da ayyukansu cikin aminci da inganci.
Wakilan masu haƙar ma’adinai daga sassa daban-daban na jihar su ma sun gabatar da jawabai tare da miƙa buƙatunsu ga Gwamna Kefas.
A yayin taron, an kuma karrama Gwamna Kefas da lambar yabo ta “Gwamnan Da Ya Fi Son Masu Haƙar Ma’adinai.”
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
