Connect with us

Labarai

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

Published

on

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423 daga filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi zuwa kasar Saudiyya.

 

Da yake kaddamar da jigilar Alhazan na farko, mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima, ya ce duk da tabarbarewar tattalin arzikin da kasar nan ta shiga saboda faduwar darajar Naira, shugaba Tinubu ya bayar da Naira biliyan 90 domin tallafa wa aikin hajjin bana.

 

Mataimakin shugaban kasar, ya bukaci maniyyatan da su dage da yi wa  shugabanninsu da malaman  addini da ma al’umma baki daya addu’a domin kawo karshen matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Yayin da yake shawartar mahajjatan da su gudanar da ayyukansu kamar yadda dokokin hukumomin Saudiyya suka tanadar, mataimakin shugaban kasar ya yabawa Gwamna Nasir Idris bisa yadda ya bayar da dukkanin goyon bayan da ya dace wajen tabbatar da nasarar  tashin jirgin farko daga jiharsa.

 

A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris na jihar ta Kebbi ya ce, a shekarar da ta gabata an yi jigilar Alhazan jihar zuwa kasa mai tsarki ne daga Sakkwato, sakamakon wasu matsaloli da aka samu a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbin, inda ya bayyana cewa a halin yanzu an shawo kan matsalar, za kuma a ci gaba da  jigilar Alhazan jihar.

Daga nan sai ya umurci masu rike da mukaman siyasa da shugabannin kananan hukumomi da su bayar da tallafin kudi ga maniyyatan mazabarsu a lokacin da suke kasa mai tsarki domin su samu damar gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali.

Shi ma da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana aikin Hajji a matsayin ibada da mutum zai tsarkake zuciyarsa, don haka ya bukaci Alhazan da kada su dauki haramtattun kayayyaki da kayan da za su hana su cimma manufar. aikin hajji.

Tun da farko a jawabinsa shugaban Hukumar Alhazai ta kasa Jalal Ahmad Arabi, ya ce hukumar ta samar da mafi kyawun masauki a Madina domin jin dadin Alhazai baya ga yin tsare-tsare masu muhimmanci tsakanin hukumomin Saudiyya da hukumar domin jin dadinsu.

Abdullahi Tukur

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara