Ilimi
Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Likitocin Da Su Duba Lafiyar Mahajjatan Bana A Saudiyya
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da tawagar likitocin guda 10, inda ya bukaci kungiyar da ta yi aiki da gaskiya, hakuri, da jajircewa wajen yi wa alhazan jihar hidima a kasar Saudiyya.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce aikin amana ce da bai kamata kungiyar ta dauka da wasa ba.
Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da wannan tawagar, inda ya nuna cewa, wannan shi ne karon farko da jihar ke tura ma’aikatan lafiya irin wannan aikin zuwa kasashen waje.
Ya jaddada godiya na zabarsu da kuma bukatar kare jin dadin alhazan Jigawa a duk tsawon wannan lokaci na aikin Hajji.
A nasa jawabin shugaban kwamitin yada labarai Abdulrashid Yusuf ya yi kira ga ‘yan wakilan da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin himma tare da sanin ya kamata da kuma tsoron Allah.
Yusuf, ya yabawa gwamnatin jihar bisa kara adadin ma’aikatan lafiya zuwa 10.
USMAN MZ
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
