Ilimi
Birnin Kudu Za Ta Samar Da Cibiyar Horas Da Maniyata
Karamar Hukumar Birnin Kdu tace tana nazarin samar da cibiyar horas da maniyyata aikin hajji ta dindindin a yankin domin karawa mahajjata kaimi wajen gudanar da aikin karbabbe.
Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin a lokacin rufe bitar da aka shiryawa maniyyatan yankin na Birnin kuudu.
Yana mai cewar, idan aka samar da cibiyar zata kunshi dukkanin muhimman wuraren da ake ziyarta a lokacin gudanar da aikin hajji.
Alhaji Muhammad Uba, yace za a kuma samar da ajujuwan horas da maniyyata da ofisoshin malaman bita da sauran dukkan abubuwan daya dace a cibiyar.
Kazalika, Shugaban Karamar Hukumar, ya biya malaman bitar alawus dinsu na wannan shekarar da ma kwanton na shekarar da ta gabata wanda ya gada daga gwamnatin da ta gabata.
A don haka, ya bukaci maniyyatan yankin su gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya mai dorewa da karuwar arziki ga yankin da jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
A jawabin da ya gabatar, jagoran malaman da suka gabatar da bitar Malam Suleiman Datti ya bukaci shugaban Karamar Hukumar ya taimaka wajen kara yiwa malaman bitar rijista a yankin.
Wasu daga cikin maniyyatan sun bayyana gamsuwa dangane da yadda Karamar Hukumar ta dauki nauyin ciyar da su na tsawon wata guda baya ga sauran hidimomin da aka yi masu.
Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, fiye da maniyyata dari ne zasu gudanar da aikin hajjin bana daga karamar Hukumar ta Birnin kudu.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
