Ilimi
Majalisar Jihar Kaduna Ta Zartas da Dokar Sabon Kudiri Kan Kwalejin Nuhu Bamalli, Ta Soke Na 1989
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da wani kudirin doka da ya soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna ta shekarar 1989, tare da maye gurbin ta da dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli.
Kudirin, mai taken “Kudirin Soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna na Shekarar 1989 (Dokokin Jihar Kaduna na Shekarar 1991) da kuma Kafa Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, 2025,” an amince da shi ne yayin zaman majalisar wanda Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya jagoranta.

Yusuf Liman ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta bai wa kwalejin damar yin gogayya da sauran manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan, tare da dacewa da tsarin karatu na zamani. Ya jaddada muhimmancin sabunta tsarin dokar duba da yadda kwalejin ke samar da kwararrun dalibai masu nagarta.
Tunda farko da Yake gabatar da rahoto akan Kudirin dokar, Shugaban Kwamitin Hadin Giwa na Ilimi da Shari’a na majalisar, Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, ya ce sun gudanar da bincike mai zurfi tare da tuntubar masu ruwa da tsaki, kuma suka gano cewa tsohuwar dokar ba ta dace da tsarin zamani ba.
Barrister Isma’ila ya ce sabuwar dokar ta kunshi muhimman sauye-sauye kamar mayar da wa’adin shugabancin makarantar zuwa shekara biyar kacal ba tare da sabuntawa ba, maimakon tsohon tsarin wa’adin shekara biyu da za a iya sabunta.
Yace wannan doka ta dace da tsarin ilimin manyan makarantu na kasar nan musamman a bangaren fasaha da kere-kere don cigaba mai maana.
Shima da Yake tsokaci Bayan amincewa da kudirin ya zama doka, Barr. Emmanuel Kantiyok, wanda ya dauki nauyin gabatar kudirin, ya yaba da yadda majalisar ta amince da dokar, yana mai cewa sabuwar dokar za ta bayar da ginshikin doka mai karfi ga ci gaban kwalejin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sauye-sauyen da dokar ta tanadar sannu a hankali don inganta tsarin ilimi a Jihar Kaduna.
Ya ce, daga yanzu, duk wanda ke rike da takardar shaidar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli yana da cikakken kariya da amincewa karkashin tanadin doka.
Shamsuddeen Mannir Atiku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
