Kasuwanci
Majalisar Neja ta Amince da Dokar Hana Ayyukan Baban Bola a Unguwanni
Daga Aliyu Lawal
Majalisar Dokokin Jihar Neja ta amince da kudirin dokar daidaita ayyukan Baban bola da masu kasuwancin karafa da aka fi sani da ‘yan gwangwan a cikin Unguwanni.
An amince da kudirin dokar ne yayin zaman majalisa da aka gudanar a harabar majalisar da ke Minna.
Amincewar ta biyo bayan gabatarwa da kuma karɓar rahoton hadin gwiwar kwamitocin majalisar kan Muhalli da Sauyin Yanayi, Shari’a da Harkokin Doka.
Yayin gabatar da rahoton, shugaban kwamitocin hadin gwiwa, Mohammed Garba, mai wakiltar mazabar Agwara, ya bayyana cewa kwamitocin sun gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a inda suka gayyaci masu ruwa da tsaki domin gabatar da nasu ra’ayoyin.
Ya ce an gudanar da wannan tattaunawa ne sakamakon karuwar damuwa kan barazanar tsaro, illa ga muhalli, da matsalolin zaman lafiya da suka shafi ayyukan baban bola da kasuwancin karafa ba tare da tsari ba a cikin unguwanni a fadin jihar.
Rahoton ya nuna cewa an tsara kudirin dokar ne domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, inganta tsaron jama’a, da kuma tsara harkokin sana’ar karafa da “Panteka” ta hanyar mayar da su wurare na musamman da aka ware a wajen unguwannin.
Haka kuma kwamitocin sun lura cewa ayyukan wadanda aka fi sani da Baban bola da ‘yan kasuwar karafa na da alaka da karuwar sace-sace da lalata kadarorin gwamnati da na jama’a.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
