Labarai
Jihar Neja Ta yi Sahu 2 na Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
Daga Aliyu Lawal
HJimillar Maniyyata dari shida da casa’in daga jihar Neja ne ya zuwa yanzu aka yi jigilarsu zuwa daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu da ke Minna zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja, Jibrin Usman Kodo, ya sanya wa hannu kuma ya fitar ga manema labarai a Minna.
Sanarwar ta bayyana cewa rukuni na farko ya tashi ne ranar Litinin 11 ga watan Mayun 2026 a jirgin saman Flynas na ƙasar Saudiyya, daga Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu da ke Minna, yayin da rukuni na biyu ya tashi jiya, 12 ga watan nan, lamarin da ke nuna ci gaba cikin nasara na jigilar maniyyatan Hajjin bana da hukumar ke gudanarwa.
Jibrin Usman Kodo ya bayyana cewa rukuni na biyu ya ƙunshi wasu maniyyata daga ƙananan hukumomin Chanchaga da Mashegu da Kontagora da Rijau da Borgu, kuma sun tashi da misalin ƙarfe 6:34 na yamma agogon Najeriya kamar yadda kamfanin Flynas mai kula da jigilar ya tsara.
Ya ce hakan wata alama ce da ke nuna yadda gwamnatin Gwamna Mohammed Umar Bago ta bai wa jin daɗin maniyyata muhimmanci, inda gwamnan ya halarci kaddamar da tashin jirgin farko domin yi wa maniyyatan bankwana.
Wannan ya kawo jimillar maniyyatan da aka kai Saudiyya zuwa 690 daga cikin kujeru 2,281 da aka ware wa jihar, yayin da ake sa ran jirgi na uku zai tashi ranar Alhamis 14 ga watan nan.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
