Connect with us

Labarai

An Yi wa Yara Sama da 66,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Tarauni

Published

on

Daga Khadijah Aliyu

Yara kimanin 66,446 ne  aka yi wa rigakafin cutar shan inna wato polio, a  Karamar Hukumar Tarauni, wanda hakan ya zama babbar nasara a ƙoƙarin da ake yi na kawar da cutar baki ɗaya.

Mai kula da harkokin lafiya na matakin farko a yankin, Muktar Datti Gwarzo, ya danganta wannan nasara da goyon bayan al’umma da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki.

Ya bayyana cewa jajircewar shugabannin gargajiya, ma’aikatan lafiya, da shugabannin ƙaramar hukuma ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa an yi wa dukkan yaran da suka cancanta wannan rigakafi.

Gwarzo ya ƙara da cewa za a ci gaba da ƙarfafa wayar da kan jama’a domin ilmantar da su muhimmancin yin rigakafi a kai a kai, da nufin kawar da cutar polio gaba ɗaya a yankin.

Shi ma da yake jawabi, mai wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya, Musa Abdullahi Shamakawa, ya yaba da ƙwazon ma’aikatan lafiya da sarakunan gargajiya wajen wayar da kan iyaye kan amfanin rigakafi.

A nasa bangaren, Daraktan kula da ma’aikata na ƙaramar hukuma kuma Shugaban Ƙungiyar Daraktocin Ƙananan Hukumomi 44, Tijjani Madaki Gulya, ya buƙaci iyaye da masu kula da yara da su ci gaba da goyon bayan shirye-shiryen rigakafi domin kare lafiyar yara da al’umma baki ɗaya.

Ya jaddada cewa ci gaba da shiga irin waɗannan shirye-shirye yana da matuƙar muhimmanci wajen hana yaduwar cututtukan da za a iya rigakafinsu.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara