Labarai
Kano: CDA Ta Raba Tan 2.85 Na Ingantattun Iri
Daga Khadijah Aliyu
Cibiyar bincike kan inganta noma a yankunan da ke da ƙarancin ruwa ta Jami’ar Bayero Kano(CDA), ta raba tan 2.85 na ingantattun iri ga manoma daga ƙauyuka 22 da wasu biyar, domin ƙara yawan amfanin gona da inganta wadatar abinci a Arewacin Najeriya.
An yi rabon ne a taron masana da manoma da masu zuba jari karo na 4 da aka gudanar a Jami’ar Bayero.
Irin da aka raba sun haɗa da wake, masara, gero, dawa, waken soya da shinkafa. Ƙananan ma’aikata ma sun amfana domin inganta samar da abinci a gidajensu.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Haruna Musa, ya ce taron na haɗa bincike da aikace-aikacen noma domin inganta samar da abinci.
Daraktan CDA, Farfesa Sanusi Gaya Mohammed, ya ce shirin na taimaka wa manoma wajen ƙara yawan amfanin gona da jure sauyin yanayi.
Manoma sun nuna godiya, suna cewa tallafin ya taimaka wajen inganta noma da rayuwarsu.
An kuma gudanar da baje kolin sabbin fasahohin noma tare da halartar hukumomi da kamfanoni daban-daban.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
