Labarai
Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 835 Don Sayen Kayan Agajin Gaggawa Saboda Ambaliya
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sayen kayayyakin agajin gaggawa na shirin tunkarar ambaliya da mayar da martani na shekarar 2026, kan kuɗi sama da naira miliyan 835.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga Rediyon Najeriya a Dutse.
Ya ce, kayayyakin da aka amince a saya sun haɗa da muhimman kayan abinci na gaggawa, kayan sawa, da kuma kayan gini, domin tabbatar da gaggawar taimako idan ambaliya ta auku a sassan da ke cikin haɗarin ambaliya a jihar.
Ya bayyana cewa, amincewar majalisar zartarwa ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) na da nufin tabbatar da cewa za a tanadi waɗannan kayan agaji a wurare masu muhimmanci domin a iya kai su cikin gaggawa duk lokacin da bukata ta taso.
Ya ƙara da cewa, kayan abinci za su taimaka wajen magance bukatun gaggawa na abinci ga mutanen da ambaliya ta raba da muhallansu, yayin da kayan sawa da na gini za su bayar da muhimmin tallafi ga iyalan da iftila’in ambaliya ya shafa.
Sagir ya jaddada cewa, gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna jihar, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da ke fuskantar haɗarin ambaliya, da su ci gaba da bin shawarwarin tsaro da hukumomin da abin ya shafa ke bayarwa.
Ya kuma bukaci jama’a da su nuna haɗin kai da goyon baya ga hukumomin agajin gaggawa idan irin wannan iftila’i ya faru.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
