Ilimi
Zamfara Ta Amince Da Shirin Gaggawa Na Kwana 120 Domin Farfaɗo Da Ilimi
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da wani shirin gaggawa na kwanaki 120 da nufin magance manyan matsalolin da ke addabar ɓangaren ilimi a jihar.
An ɗauki wannan mataki ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 65, wanda gwamnan ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ilimi, lafiya, ayyuka da sauran fannoni, inda aka amince da manyan tsare-tsare domin inganta ayyukan gwamnati a jihar.
Ya ce babban abin da ya fi jan hankali a taron shi ne amincewa da shirin farfaɗo da ilimi, wanda ya samo asali daga binciken da Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Tabbatar da Ingancin Ilimi suka gudanar a baya.
A cewarsa, kwamishinan ilimi mai kula, Abdulmalik Abubakar Gajam, ne ya gabatar da shirin, wanda ya ƙunshi sauye-sauye na musamman cikin ƙayyadadden lokaci.
Shirin ya haɗa da tantance albashin ma’aikata, cikakken nazarin makarantu, da duba gine-ginen makarantu, tare da mayar da hankali kan inganta shugabanci da amfani da fasahar zamani, horar da malamai, da kuma kula da jin daɗin ɗalibai.
Haka kuma, majalisar ta amince da kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa domin gano da kuma tantance gine-ginen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a kusa da makarantu.
Sanarwar ta ce za a bai wa wannan kwamiti, wanda Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha za ta jagoranta, ikon cire ko matsar da irin waɗannan gine-gine domin samar da ingantaccen muhalli na karatu.
Bugu da ƙari, majalisar ta amince da ƙirƙirar dokar bai ɗaya da za ta shafi dukkan matakan ilimi daga kula da yara ƙanana har zuwa manyan makarantu.
An tsara wannan doka ne tare da haɗin gwiwar manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da abokan hulɗa na ci gaba, kuma za a miƙa ta ga majalisar dokokin jihar domin duba ta da kuma amincewa da ita cikin lokacin shirin gaggawar.
A matsayin wani ɓangare na gyare-gyaren da ake yi, kakakin gwamnan ya ƙara da cewa gwamnan ya amince da sauya wurin aiki ga ma’aikatan da ba malamai ba, kamar masu aike-aike, ma’aikatan tsafta, masu kula da lambun makaranta, masu girki, masu gadi, direbobi da ƙwararru, daga jerin albashin Ma’aikatar Ilimi zuwa wasu ma’aikatu ko kamfanoni masu zaman kansu.
Haka kuma, majalisar ta amince da kafa kwamitin jagoranci na jihar kan dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, tare da ba shi damar kafa ƙungiyar masu fasaha domin taimakawa aiwatar da shirin.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
