Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Jigawa ta Sami Gagarumin Cigaba a Bangaren Ilimi- Gwamna Namadi

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce jarin da take ci gaba da zubawa a bangaren ilimi ya fara haifar da sakamako mai kyau, musamman a matakin ilimin firamare a fadin jihar.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan  yayin da ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki a bangaren ilimin firamare, wanda aka shirya domin duba irin ci gaban da aka samu, kalubalen da ake fuskanta da kuma damar da ke akwai.

 

An gudanar da taron ne a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

Gwamna Namadi ya nuna jin dadinsa da sakamakon taron, yana mai cewa bayanan da aka gabatar sun nuna tasirin jarin da gwamnati da abokan hulda ke zubawa a bangaren ilimi.

Ya ce gudummawar hukumomin bada tallafi da sauran abokan hulda, tare da kokarin gwamnati, na taimakawa matuka wajen inganta ilimi a fadin jihar.

Gwamnan ya yaba da jajircewar abokan hulda wajen inganta koyarwa da koyo. Haka kuma ya ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiki tare da su, da kuma samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi nazari kan dukkan shawarwari da gudummawar da aka bayar a taron, domin duba yiwuwar shigar da su cikin tsare-tsare da manufofin ilimi na jihar.

A nasa bangaren, Kwamishinan Ilimin Firamare, Dakta Lawal Yunusa Danzomo, ya bayyana cewa taron ya hada dukkan sassa da cibiyoyin da ke da alaka da tattara bayanan ilimi da kuma gudanar da ayyukan ilimi.

Ya jaddada cewa magance matsalolin bangaren ilimi na bukatar hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.

Danzomo ya kara da cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa kowanne yaro a Jigawa ya shiga makaranta, tare da wucewa  zuwa mataki na gaba ba tare da yankewa ba.

Ya ce binciken da aka yi a baya-bayan nan ya nuna an samu ci gaba wajen shigar yara makaranta, da ci gaban karatunsu zuwa  mataki na gaba da kuma yawan wadanda ke kammala karatu. Haka kuma an samu ci gaba wajen daukar malamai aiki, turasu wuraren aiki, horas da su, halartar aiki, da kuma ingancin koyarwarsu.

Taron na daga cikin kokarin Gwamna Umar Namadi na farfado da bangaren ilimi da kuma mayar da shi ginshikin ci gaban al’umma a Jihar Jigawa.

Daga cikin kungiyoyi da abokan hulda da suka halarci taron akwai PLANE, AGILE, UNICEF, Bankin Raya Kasashen Musulmi (IDB), da Save the Children, da sauransu.

 

 

Labarai

Labarai15 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai17 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara