Ilimi
Farfesa Gumel Ya Fitar da Sabon Tsari da Zai Daga Martabar FUD
Daga Usman Muhammad Zaria
Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD), Farfesa Ahmad Mohammed Gumel, ya bayyana cikakken shiri da zai sauya jami’ar zuwa cibiyar bincike, kirkire-kirkire da kuma ingantaccen ilimi a Najeriya nan da shekarar 2030.
Farfesa Ahmad Gumel ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da manufofinsa lokacin da ya karɓi ragamar aiki a hukumance a matsayin Shugaban jami’ar na huɗu.

Ya jaddada muhimmancin samar da ɗaliban da ke da ƙwarewa, nagarta da kuma bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban ƙasa.
A cewarsa, wannan shirin sauyi yana tafiya ne bisa wani tsarin bunƙasa jami’a mai manufofin goma sha ɗaya, inda aka fi bai wa fannonin inganta ilimi, bincike da kirkire-kirkire, bunƙasa fasahar zamani, da inganta jin daɗin ɗalibai da ma’aikata muhimmanci.


Ya bayyana cewa jami’ar za ta sabunta tsarin karatunta domin ya dace da ƙa’idojin Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da kuma kyawawan ƙa’idojin ilimi na duniya, tare da shirin ƙaddamar da sabbin shirye-shiryen karatu kamar Fasahar Basirar Na’ura (Artificial Intelligence), Kimiyyar Bayanai (Data Science), Cloud Computing, Noman da ya dace da sauyin yanayi (Climate-Smart Agriculture), da sauran sabbin fannoni.

Shugaban jami’ar ta FUD ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa an tsara cikakken shirin bunƙasa jami’ar na shekaru biyar, wanda nan ba da jimawa ba za a gabatar da shi ga majalisar gudanarwa domin amincewa.
-
Labarai6 days agoRamadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsaro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoKaramar Hukumar Birnin Kudu ta Nemi Hadin Kan Kungiyar ‘Yan Achaba Wajen Dakile Matsalar Tsaro
-
Labarai5 days agoSojojin Najeriya Sun Karɓi Motocin Yakin Da Aka Kera A Cikin Ƙasa
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kano Ta Fara Shari’ar Tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam
-
Labarai2 days agoRanar Mata Ta Duniya: Gwamnatin Kano Ta Bukaci A Kara Tallafa wa Mata da ’Yan Mata
-
Labarai5 days agoTsarin Kundin Shirin Bunkasa Samarda Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai6 days agoKungiyoyin Alumma a Jigawa Sun Bayyana Goyon Bayansu ga Gwamna Namadi Kan Lamarin Walida Abdulhadi
-
Labarai4 days agoGwamnatin Zamfara Ta Ayana Dokar Ta-baci Kan Shan-Inna a Karamar Hukumar Gummi
