Ilimi
Farfesa Tukur Adamu Ya Fara Aiki a Matsayin Shugaban Jami’ar Tarayya Gusau na Hudu
Daga Aminu Dalhatu
Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) Farfesa Tukur Adamu ya yi alƙawarin inganta ilimi, bincike, ƙirƙire-ƙirƙire, walwalar ɗalibai da ma’aikata.
Farfesa Tukur Adamu wanda ya gaji Professor Mu’azu Gusau Abubakar bayan kammala wa’adinsa na shekaru biyar, ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi ragamar shugabancin Jami’ar a matsayin shugabata na huɗu.
Sabon Shugaban ya ce zai mayar da hankali kan binciken da zai magance matsalolin al’umma, kamar yadda ya yi a UDUS.
Ya kuma yi alƙawarin haɗa kai da gwamnatin Zamfara, Sarakuna, Jami’an tsaro da ƙungiyoyin addini domin ci gaban jami’ar.
An naɗa shi ne a taron Majalisar Gudanarwar jami’ar a watan Disamba 2025.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
