Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Kamun Kifi da Al’adu na Argungu

Published

on

Daga Sani Haruna Dutsinma

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bukaci mazauna jihar da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kyakkyawar tarba tare da nuna  farin ciki yayin ziyararsa zuwa jihar a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairun 2026.

Malam Yahaya Sarki, Mashawarci na  Musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi kan Harkokin Yada Labarai ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar domin bude wasu manyan ayyuka da gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta aiwatar, tare da halartar bikin al’adu da kamun kifi na Argungu karo na 61 wanda ya fara a yau Laraba 11 ga watan Fabrairun 2026.

Kwamishinan Harkokin Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmed, ya roki hadin kan al’ummar jihar, yana mai jan hankalin su da su bayyana kyakkyawan dabi’un su ga manyan baki daga ƙasashen duniya.

Sanarwar ta bayyana cewa ayyukan da Shugaban ƙasa zai bude sun haɗa da Sakatariyar Gwamnati da aka sawa suna Bola Ahmed Tinubu, da babbar tashar motar Birnin Kebbi, da sababbin hanyoyi a cikin birni, da tagwayen hanyoyi na Argungu, da sauransu, kafin ya halarci bukukuwan al’adun.

Haka kuma, za a rufe  wasu hanyoyi a cikin Birnin Kebbi da wasu sassan Argungu  na ɗan lokaci domin sauƙaƙa zirga-zirgar shugaban ƙasa bisa ƙa’idojin tsaro, sannan an bukaci al’umma da su kasance masu bin doka, zaman lafiya, da nuna kyawawan ɗabi’u.

 

 

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara