Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Ja Hankalin Maniyyata Game da Muhimmancin Halartar Taron Bita

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudirinta na ci gaba da ilimantarwa tare da wayar da kan maniyyata aikin Hajjin bana.

Darekta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Yana mai cewar ilimantarwa tare da wayar da kan maniyyatan jihar na daya daga cikin abubuwan da hukumar ta sanya a gaba domin samun nasarar da ta dace.

Ya kara da cewar, hukumar tana da malaman bita da za su taimaka wa maniyyatan wajen sauke farali a kasar Saudiyya.

A don haka, Labbo ya bukaci maniyyatan da su maida hankali wajen halartar wuraren bita a kananan hukumomin su.

Ya yi nuni da cewar, halartar taron bitar zai kara musu ilimin sanin yadda za su gudanar da aikin hajji karbabbe gami da
baiwa maniyyatan damar samun sakonni dake fitowa daga hukumar dangane da shirye-shiryen da suka shafi aikin Hajji.

Darekta Janar din ya bayyana cewar, tuni hukumar ta fara tantance lafiyar maniyyatan a ci gaba da shirye-shiryen da take yi.

Ya yabawa Gwamna Umar Namadi da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suke baiwa hukumar a kowane lokaci domin cimma burin da aka sanya a gaba.

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara