Labarai
Ma’aikatan Lafiya na BKD-HEALTH Sun Karrama Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatan lafiya na BKD-HEALTH sun karrama shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, bisa shugabanci nagari da kuma daukar matasa aiki.
A jawabinsa na maraba, jagoran ma’aikatan na BKD-HEALTH Nasiru Sanusi ya ce taron ya dace da cikar su shekara daya da samun wannan aiki wanda ma’aikata 210 ke samun alawus ba tare da yankewa ba.

A sakonsa na fatan alkairi, shugaban sashen kula da tsaftar ruwa da muhalli na karamar hukumar ta bakin Malam Saminu Musa, ya ce baya ga daukar ma’aikatan BKD-HEALTH domin inganta aikin lafiya, shugaban karamar hukumar yana kashe naira milyan 5 duk wata wajen tallafawa marasa lafiya da kudaden magani.
Shi ma a nasa jawabin, Kansilan ayyuka Alhaji Haladu Maigari, ya ce cikin watanni da kama mulkinsa, shugaban karamar hukumar ya gyara asibitoci guda 7.

Ya kuma jinjinawa ma’aikatan na BKD-HEALTH bisa lura da kokarin shugaban karamar hukumar, inda ya yi addu’ar nan gaba za a ba su aiki na dindindin.
Wasu daga cikin ma’aikatan na BKD-HEALTH Sulaiman Yusuf, Ai’sha Isma’il Sulaiman da Ummu Salma Abdullahi sun ce sun kwashe shekara da shekaru a matakin aikin sa kai da na wucin gadi.
Sun kuma godewa shugaban karamar hukumar bisa samun wannan dama.
Da ya ke mayar da jawabi, shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba ya bukaci ma’aikatan na BKD-HEALTH da su rike ayyukan su bisa gaskiya da Amana domin kuwa karin alawus din su zai dogara akan kwazo da mutunta aiki.
Ya bayyana taron a matsayin cikakkiyar sheda kan abubuwan da ke wakana a karamar hukumar Birnin Kudu.

Builder, ya yi kira ga jama’ar yankin da su shiga a dama da su wajen yankar katin zabe da na jam’iyar APC domin ciban yankin.
Sauran wadanda aka karrama tare da shugaban karamar hukumar sun hadar da Alhaji Haladu Maigari da Alhaji Ibrahim Isyaku da Malam Muhammad Musa Badamasi da Mai kula da shirin BKD-HEALTH, Mujittafa Ibrahim.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
