Ilimi
Gwamna Lawal Ya Bada Umarnin Gyaran Makarantun Zamfara
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna matuƙar damuwa kan halin da wasu makarantun gwamnati ke ciki a ƙaramar hukumar Gusau, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya kai ziyarar duba wasu makarantu tare da mai rikon mukamin Kwamishinan Ilimi na jihar, Abdulmalik Gajam, da sauran jami’an gwamnati.

Ya ce yawancin ababen more rayuwa da aka gani sun lalace tsawon shekaru, kuma suna buƙatar gyara cikin gaggawa.
A cewarsa, halin da makarantu ke ciki a cikin babban birnin jihar abin damuwa ne, yana mai cewa a yankunan karkara lamarin na iya zama mafi muni.

Gwamnan ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin kowace al’umma, yana mai cewa ba za a samu ci gaba mai ma’ana ba tare da ingantaccen tsarin ilimi ba.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da zaɓen makarantu 20 domin a yi musu cikakken gyara cikin watanni huɗu, wanda zai haɗa da gyaran gine-gine, samar da kayayykin koyo da koyarwa, da horas da malamai.

Haka kuma, ya ce an kafa kwamiti a ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi domin tantance matsalolin da kuma samar da hanyoyin magance su, inda za a fara aiwatar da shirin nan take.
Gwamnan ya yi kira ga malamai, ɗalibai da al’umma da su riƙa kula da kadarorin makarantu tare da kare su daga ɓarna, domin hakan abu ne da ya rataya akan kowa.

A nata ɓangaren, Mai kula da shirin ilimin yara mata na AGILE a jihar, Hajiya Sa’adatu Abdu Gusau, ta ce tabarbarewar ilimi matsala ce da ta daɗe, tana mai kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa domin magance ta.
Hakazalika, Gwamnan ya kuma duba tashar ruwa ta Gusau domin inganta samar da ruwa a jihar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
