Labarai
Zaɓin Jama’a, Ba Ƙarfin Jam’iyya ba, Zai Tantance Zaɓen Kauru a 2027
Zaɓen shekarar 2027 a ƙaramar hukumar Kauru a Jihar Kaduna na iya kasancewa wanda zaɓin ‘yan takara da karɓuwarsu a tsakanin al’umma zai fi rinjayar sakamakonsa, maimakon ƙarfin jam’iyya.
Wannan na kunshe ne a cikin wani rahoto da ƙungiyar Matasan Kauru ta fitar, inda ta bayyana cewa dogaro kawai da tsarin jam’iyya ko hukuncin kotu ba zai tabbatar da nasarar zaɓe ba.
Ƙungiyar ta ce sakamakon zaɓen 2023 a mazaɓar tarayya ta Kauru ya nuna ƙuduri da zaɓin da masu kaɗa ƙuri’a suka yi a faɗin yankin.
A cewar ƙungiyar, yawan fitowar masu zaɓe da kuma yadda aka kaɗa ƙuri’a iri ɗaya a mazaɓu daban-daban ya nuna wata ƙwaƙƙwarar akidar siyasa daga al’umma, ba wai canjin ra’ayi na ɗan lokaci sakamakon kamfen ba.
Rahoton ya ƙara da cewa daga Kauru ta Yamma zuwa Makami, sannan daga Geshere zuwa Kwassam, masu zaɓe sun nuna tsari iri ɗaya wajen kaɗa ƙuri’a, wanda ke nuna cewa sun yanke shawara ne bisa muradunsu da bukatun yankin.
Rahoton ya bayyana wannan yanayin zaɓe a matsayin tsari mai ma’ana da nufin nuna ikon dimokuraɗiyya na jama’a.
Duk da cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Kauru a yanzu, Mukhtar Chawai, ya sake samun kujerarsa ta hanyar hukuncin kotu, KYA ta jaddada cewa hukuncin kotu ya bambanta da irin umarnin da masu zaɓe suka bayar a akwatin zaɓe.
Ƙungiyar ta kuma lura cewa yanayin siyasar Kauru ya fara sauyawa, inda ake samun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, haka kuma wasu daga APC da Labour Party (LP) suna komawa African Democratic Congress (ADC), lamarin da ke nuna fara tsara dabarun siyasa tun kafin zaɓen 2027.

Excerpt from the 2023 INEC
Sai dai duk da waɗannan sauye-sauye, KYA ta ce ra’ayin masu zaɓe yana nan daram, domin abin da ke rinjayar su shi ne aiki, yadda jama’a ke kallon ɗan takara da kuma kusancinsa da al’umma, ba wai jam’iyyarsa kaɗai ba.
Rahoton ya ƙara da cewa ko da yake APC na da fa’idar kasancewa jam’iyya mai mulki, rikicin cikin gida tsakanin masu neman takara na iya zama babban ƙalubale.
Ƙungiyar ta bayyana cewa idan Mukhtar Chawai ya sake tsayawa takara, hakan na iya zama haɗari a siyasance, idan aka yi la’akari da yadda aka kaɗa ƙuri’a a 2023.
Har ila yau, ƙungiyar ta ce jam’iyyun PDP da ADC suna shirin fitar da ‘yan takara masu ƙarfi, inda PDP ke dogaro da Karɓuwar ta abaya na magoya baya, yayin da ADC ke ƙara samun karɓuwa sakamakon sababbin masu sauya sheƙa da kuma ƙuri’un nuna rashin gamsuwa.
Yusuf Zubairu Kauru
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
