Labarai
Zaben 2027: INEC Ta Ƙarfafa Shiri Da Tsarin “Zero-Failure” Ta Raba Sabbin Motoci
Daga Abdullahi Shettima,
Kaduna
Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, ta ce tana kara kaimi wajen shirye-shiryen gudanar da Babban Zaben 2027, ta hanyar bullo da wani sabon tsarin ayyuka da dabarun jigilar kayan zabe da nufin kauce wa duk wani cikas a ranar zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Joash O. Amupitan, ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Kaduna, yayin taron tuntubar ma’aikatan hukumar na shiyyar Arewa maso Yamma da kuma tantance shirye-shiryen Babban Zaben 2027.
Farfesa Amupitan ya ce hukumar na amfani da tsarin “Zero-Failure”, wato tsarin da ba zai amince da gazawa ba, wanda ya shafi jigilar kayan zabe da kai su wuraren da za a yi amfani da su tun da wuri, daidaita ayyukan jami’an tsaro da kuma horas da ma’aikatan wucin gadi da za su gudanar da zabe.
Ya sanar da cewa hukumar ta fara saye da raba sabbin motocin daukar kaya ga ofisoshin INEC na jihohi da kananan hukumomi a fadin kasar.
A cewarsa, rabon motocin zai inganta zirga-zirgar jami’an zabe, tsaron su da kuma ingancin ayyukansu a wurare daban-daban.
Shugaban INEC din ya kuma ce hukumar na inganta fasahohin zabe, ciki har da tsarin tantance masu kada kuri’a da kuma aika sakamakon zabe, domin rage matsalolin fasaha yayin zaben 2027.
Ya ce ana kuma duba sabon tsarin eEC8A Result Management System, domin tabbatar da cewa yadda sakamakon zabe ke tafiya daga rumfunan zabe zuwa cibiyar tattara sakamakon kasa yana kasancewa a bayyane, ana iya tantance shi kuma ana tabbatar da ingancinsa.


Farfesa Amupitan ya bayyana rashin sha’awar kada kuri’a, raguwar amincewar jama’a da tsarin zabe, yada labaran karya da kuma bayanan bogi a matsayin manyan kalubalen da ke fuskantar tsarin zabe.
Ya gargadi jami’an zabe cewa rashin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ciki har da makara wajen bude rumfunan zabe, nuna bangaranci da kuma gazawar sanar da jama’a matsalolin fasaha yadda ya kamata, na iya kara rage amincewar jama’a da zabe.
Saboda haka, Shugaban INEC ya umurci ma’aikatan hukumar da su tabbatar da tsaka-tsaki, kwarewa da kuma bin tanade-tanaden Dokar Zabe da ka’idojin hukumar.
Ya ce sahihancin zaben 2027 ba zai dogara kawai kan fasaha da dokoki ba, har ma da yadda jami’an zabe za su aiwatar da dokokin yadda ya kamata tun daga matakin kasa har zuwa matakin kananan hukumomi da rumfunan zabe.
Za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘Yan Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaben Gwamnoni da ‘Yan Majalisun Dokokin Jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
