Labarai
Kashim Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Zuwa Kebbi
Daga Sani Dutsinma
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci wata babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Jihar Kebbi domin yin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar bisa rasuwar Shugaban Majalisar Dokoki ta Jiha, Muhammad Usman Zuru, da kuma hare-haren ‘yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Shanga.
Ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana abubuwan da suka faru a matsayin babban rashi ga Jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya. Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayi Shugaban Majalisa, ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Shettima ya kuma nuna alhini kan hare-haren da aka kai ƙauyukan Gebe, Kalkami, Tungar Rimi da Awaye, wanda ya haddasa asarar rayuka da lalata dukiya, ciki har da sojoji goma sha ɗaya da suka rasa rayukansu yayin aikin tsaro.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya, ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, za ta tallafa wa waɗanda suka rasa matsugunansu tare da samar da agaji ga al’ummomin da abin ya shafa.

Mataimakin shugaban ƙasa ya kuma yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa ƙoƙarinsa wajen ci gaban ilimi, ababen more rayuwa da kuma haɗa kan al’umma a jihar Kebbi.
A nasa bangaren, Sarkin Zuru, Muhammad Sanusi Mikaili Gomo III, ya gode wa tawagar gwamnatin tarayya bisa ziyarar ta’aziyyar da tallafi ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.

Haka zalika, shi ma Gwamna Nasir Idris kuma ya gode wa Shugaba Tinubu bisa turo tawaga, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa kwamiti da kuma ware kuɗi domin sake tsugunar da waɗanda suka rasa matsugunni da kuma tallafa wa iyalan sojojin da suka rasu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
