Labarai
Rasuwar Nasiru Alhassan Babban Rashi Ne Ga Jigawa – Labbo
Daga Usman Muhammad Zaria
Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, da Amirul Hajj na jihar, Sarkin Dutse Alhaji Hamim Nuhu Muhammadu Sunusi, bisa rasuwar jami’in kula da yankin Maigatari, marigayi Nasiru Alhassan Muhammad.
A cikin saƙon ta’aziyyar da ya aike wa wakilin Rediyon Najeriya a Makkah, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa rasuwar jami’in ta girgiza shi matuƙa.Yana mai cewa wannan rashi ne da ba za a iya maye gurbinsa ba.Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalan mamacin haƙurin jure wannan babban jarrabawa.

Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo,
Ya ce marigayi Nasiru Alhassan Muhammad ya rayu ne cikin hidimtawa al’umma, kasancewarsa jajirtaccen ma’aikacin gwamnati kuma ƙwararren jami’i wanda ya sadaukar da kansa wajen yi wa Alhazai hidima a Najeriya da kuma ƙasar Saudiyya.
A cewar Ahmed Umar Labbo, rasuwar marigayin babban rashi ne ga Jihar Jigawa baki ɗaya, ba ga iyalansa, abokansa da abokan aikinsa kaɗai ba.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
