Connect with us

Labarai

Hukumar Alhazan Jigawa Ta Yi Rashin Jami’inta Bayan Dawowa Daga Aikin Hajji

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Allah Ya yi wa jami’in kula da yankin Babura, Maigatari da Sule Tankarkar na Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa, Alhaji Nasiru Alhassan Muhammad, rasuwa.

Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya tabbatar da rasuwar ga wakilin Rediyon Najeriya a Makkah.

A cewarsa, marigayi Alhaji Nasiru Alhassan Muhammad yana cikin rukuni na farko na Alhazan jihar da suka tashi daga Makkah a ranar Asabar 6 ga watan Yunin 2026, ta filin jirgin sama na Jeddah zuwa Najeriya bayan kammala aikin Hajjin bana.

Alhaji Ahmed Umar Labbo, wanda ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa da wannan rasuwa, ya ce an garzaya da marigayin zuwa wani asibiti mai zaman kansa a Dutse bayan isowarsu filin jirgin sama.

Ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga daukacin ma’aikatan hukumar Alhazai, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, abokan aikinsa, ‘yan uwansa, Sarkin Tsakar Gidan Gumel kuma Hakimin Maigatari, Sarkin Dutse, wanda shi ne Amirul Hajj na Jihar Jigawa, da kuma kwamitin harkokin addini na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.

Marigayin ya rasu ya bar mata guda ɗaya, yara huɗu da kuma ‘yan uwa da dama, ciki har da Sarkin Dawakin Tsakar Gidan Gumel kuma tsohon Sakataren Zartarwa na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Sani Alhassan Muhammad.

Rediyon Najeriya ya rawaito cewa rasuwar Alhaji Nasiru Alhassan ta jefa daukacin ma’aikatan hukumar cikin jimami da alhini.

Kafin rasuwarsa, shi ne jami’in da ke kula da yankin Maigatari na Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa.

An yi jana’izarsa ne da safiyar yau Lahadi a garin Gumel.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara