Labarai
Hukumar Alhazan Jigawa Ta Gargadi Mahajjata Kan Kayayyakin da Aka Haramta
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Jigawa ta gargadi Alhazanta da su guji ɗaukar kayayyakin da aka haramta a cikin jakunkunan hannu yayin dawowarsu Najeriya daga ƙasar Saudiyya.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya yi wannan kira a wata hira da wakilinmu Usman Mohammed Zaria a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya, yayin da ake shirye-shiryen dawowar Alhazan bayan kammala aikin Hajjin bana.
Ya bayyana cewa wajibi ne Alhazai su guji sanya kayayyaki masu kaifi a cikin jakunkunansu na hannu.
Ya ce daga cikin kayayyakin da aka haramta akwai bindigogi wasa, ko na gaske, kayayyaki masu saurin kamawa da wuta, wuƙaƙe, reza da almakashi.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma gargadi Alhaza da kada su sanya ruwan Zamzam a cikin manyan jakunkunansu, haka kuma su guji ɗaukar turare na fesawa.
A cewarsa, kowane Alhaji yana da haƙƙin samun lita biyar na ruwan Zamzam, don haka babu buƙatar sanya shi a cikin babban akwati.
Ya ƙara da cewa duk Alhajin da ya saɓa wa wannan umarni zaiɗiya jawowa kansa matsala, domin ana gano duk kayayyakin da aka haramta yayin binciken jakunkuna, kuma hukumomi za su kwace su.
Labbo ya bayyana cewa jiragen sama na da iyakar nauyin kayan da za su iya ɗauka, kuma ba za su iya ɗaukar kaya fiye da ƙa’idar da aka tanada ba.
Saboda haka, ya buƙaci Alhazan da su bi ƙa’idodin auna kaya domin tabbatar da dawowa cikin nasara da kwanciyar hankali.
Babban Daraktan ya kuma bayyana cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta amince da kamfanonin jigilar kaya domin Alhazan da ke da kayan da suka wuce ƙa’ida su yi amfani da su.
Ya tabbatar da cewa da zarar Alhazan sun isa Najeriya, za a miƙa musu manyan jakunkunansu tare da lita biyar na ruwan Zamzam ga kowane alhaji a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
