Connect with us

Labarai

Gwamna Bago Ya Umurci SEMA Ta Gaggawata Kai Tallafi ga Wadanda Iftila’in Guguwa ya Shafa a Mokwa da Bida

Published

on

Daga Aliyu Lawal

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya jajanta wa al’ummar yankunan ƙananan hukumomin Bida da Mokwa kan mummunar guguwar iska da ta lalata gine-gine, ciki har da gidaje wuraren sana’o’i.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar a Minna, babban birnin jihar, ga manema labarai.

Gwamna Umar Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin jimami da  tashin hankali.

Ya kuma bayyana cewa iftila’in ya jefa waɗanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali, yana mai jaddada musu cewa gwamnati za ta yi dukkanabin da ya dace don ganin ta saukaka musu halin da suka shiga.

Ya umarci Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.

Gwamna Umar Bago ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta rayuwar al’umma.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara