Labarai
Gwamnatin Neja za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da NBMA domin bunƙasa samar da iri
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa haɗin gwiwa da tabbatar da cewa abincin da aka canza halitta (GMOs) da sauran kayayyakin kimiyya ba su cutar da lafiya ko muhalli ba domin bunƙasa samar da iri da inganta harkokin noma a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa Darakta Janar na na hukumar NBMA, Bello Bawa Bwari, a hedikwatar hukumar da ke Jabi a Abuja.
Ya ce jihar na da babbar dama a fannin noma, inda ya bayyana cewa haɗin gwiwar na daga cikin wani shiri na noma sama da hekta dubu 60,000 domin samar da iri, auduga da masara, tare da ƙarin hekta dubu 40,000 don noman shinkafa da rake.
Gwamna Bago ya kuma nuna fatan cewa nan da shekarar 2027, jihar Neja za ta samar da iri a faɗin hekta 100,000, lamarin da zai sauya yanayin samar da abinci a ƙasar.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta zuba jari sosai a harkar amfani da injinan noma da kuma haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin bunƙasa samar da iri.
A nasa bangaren, Darakta Janar na NBMA, Bello Bawa Bwari, ya ce hukumar na jagorantar shirye-shiryen ƙasa na tabbatar da wadatar abinci da dorewar noma, tare da samar da hanyoyin ninkawa da bunƙasa iri, ciki har da na zamani.
Ya kuma jaddada cewa wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen cimma burin bunƙasa noma da wadatar abinci a Najeriya.
Aliyu Lawal/Minna
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
