Labarai
Jihar Jigawa Ta Kammala Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce rukuni na biyu kuma na ƙarshe na Alhazan jihar ya isa Madina lafiya, lamarin da ke nuna kammala jigilar dukkan aAhazan jihar cikin nasara.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a wata hira da wakilin Rediyon Najeriya Kaduna, Usman Mohammed Zaria, a Madina.
A cewarsa, an kai Alhazan rukuni na farko da na biyu wuraren tarihi a Madina bisa tsari, ciki har da Dutsen Uhud, Masallacin Ƙuba, Masallacin Kiblatayni, makabartar Al-Baki’a da sauransu.

Ya ce jami’an hukumar tare da malamai ne suka jagoranci Alhazan zuwa masallacin Manzon Allah a Madina.
Alhaji Ahmed Labbo ya ce an riga an tanadi tsarin ciyarwa na musamman domin kula da lafiyar Alhazan da ke fama da lalurar hawan jini da ciwon suga a yayin aikin Hajjin.
Ya bayyana cewa wannan wani bangare ne na matakan inganta lafiya da jin daɗin Alhazan jihar.

Haka kuma ya ce an shirya samar da abinci sau uku a kullum ga Alhazan jihar yayin zamansu a Saudiyya.
Babban Daraktan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a fara jigilar rukuni na farko na Alhazan zuwa Makkah.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
