Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Miliyoyin Naira
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da bayar da kwangilolin ayyukan kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki, da suka haura naira miliyan 550 a faɗin jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana hakan jim kaɗan bayan taron Majalisar Zartarwar Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Ya ce cikin ayyukan akwai farfaɗowa da inganta Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matakin Farko da ke Samamiya, a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, domin faɗaɗa damar samun kiwon lafiya da inganta ayyukan kula da lafiyar mata da yara.
Kwamishinan ya kuma ce majalisar ta amince da sayen katan 2,155 na abincin jinya da ake amfani da shi kai tsaye, wato RUTF, domin rarrabawa ga cibiyoyin kula da lalurar matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Sagir Musa Ahmed ya ce amincewa da ayyukan na nuna ƙudirin gwamnatin jihar na ƙarfafa kiwon lafiya na matakin farko da kuma yaƙi da matsanancin rashin abinci mai gina jiki tsakanin jarirai da sauran yara masu rauni.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
