Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da sakin Naira Biliyan 7.4 domin biyan ragowar kuɗaɗen kayan aikin noma da kuma kafa Cibiyar Ayyukan Noma, ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme (RH-NAMP).
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron majalisar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Dutse.
Ya ce amincewar za ta ƙarfafa aikin noma da injuna, da inganta damar manoma ta samun kayan aikin zamani da ayyukan tallafi.
Sagir Musa ya ce samar da kayan aikin zai ƙara wa manoma damar yin amfani da injuna wajen shirya gona da noma, inganta aiki, rage dogaro da aikin hannu, tare da ƙara yawan amfanin gona a jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta amince da kafa cibiyar haɗa ayyukan tallafa wa noma, ciki har da samar da kayan aikin noma, horar da manoma, gyaran injuna, tattara amfanin gona da ayyukan bayan girbi.
Ya ce cibiyar za ta samar da dandali na bai wa manoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma damar samun ayyukan noma da injuna, tare da samar da wurin ajiya, kula da gyara taraktoci da sauran kayan aikin noma.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai7 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Ga Ayyukan Samar Da Ruwa
-
Labarai6 days agoJigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya
-
Labarai4 days agoTinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amince Da Naira Miliyan 570 Don Inganta Abinci Mai Gina Jiki
-
Labarai5 days agoSauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi
-
Labarai13 hours agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai2 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
