Labarai
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
Daga Isma’il Adamu
Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, da wani mutum mai suna Malam Adamu a karamar hukumar Dutsin-Ma ta jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a kofar gidan malamin, jim kadan bayan kammala wani taro da aka gudanar a gidansa. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun iso ne a kan babur, inda suka bude wa malamin da almajirinsa wuta.
Dukkan mutanen biyu sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su Babban Asibitin Dutsin-Ma domin ba su kulawar gaggawa, amma daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Malam Adamu shi ne mutum na biyu da aka kashe a harin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar-Sadiq Aliyu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya ce wasu mutane biyu dauke da makamai da ke kan babur ne suka bude wa wadanda abin ya shafa wuta.
Sanarwar ta ce bayan samun rahoton harin, jami’in ’yan sanda na sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an rundunonin musamman da sauran jami’an tsaro zuwa yankin. Rundunar ta ce ta fara gudanar da bincike tare da kara kaimi wajen gano wadanda ke da hannu a aikata laifin da kuma cafke su.
Kwamishinan ’yan sandan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da mabiyansu, da kuma al’ummar karamar hukumar Dutsin-Ma.
Kashe malamin ya jefa mazauna yankin, musamman mabiyansa, cikin jimami, yayin da har yanzu ba a bayyana dalilin kai harin ba.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
