Labarai
Su Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
Wasu ’yan bindiga da ake zargi da aikata laifuka sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma ta Jihar Katsina.
An kai wa malamin harin ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ƙofar gidansa, inda maharan suka buɗe wuta a kansa da wani mutum da ke tare da shi.
Daga bisani, an garzaya da waɗanda harin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Dutsin-Ma domin ba su agajin gaggawa, amma bayan wasu mintuna aka tabbatar da rasuwarsu.
Mazauna Dutsin-Ma sun bayyana cewa sunan mutum na biyu da harin ya rutsa da shi Malam Adamu ne, wanda ake kyautata zaton cewa harin ya same shi ne bisa kuskure.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun isa wurin ne a kan babur, inda suka yi wa waɗanda abin ya shafa kwanton ɓauna jim kaɗan bayan kammala wani taro da aka gudanar a gidan Sheikh Masussuka.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakken bayani game da harin, ko su waye maharan, ko kuma dalilin da ya sa suka kai harin ba.
A halin da ake ciki, kisan ya jefa mazauna yankin cikin jimami, musamman mabiyan malamin.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa tana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata laifin domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Abubakar-Sadiq Aliyu, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa wasu mutane biyu ɗauke da makamai, waɗanda ke kan babur, sun buɗe wuta tare da raunata mutanen biyu har lahira.
Sanarwar ta ce: “Bayan samun rahoton faruwar lamarin, Jami’in ’Yan Sanda na Sashen Dutsin-Ma ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru. Nan take aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti mafi kusa domin ba su kulawar gaggawa amma abin takaici, likitan da ya duba su ya tabbatar da rasuwarsu.
“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an rundunonin musamman zuwa yankin.
“Kwamishinan ’Yan Sandan ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da abokai da mabiyan waɗanda suka rasu, da kuma al’ummar Ƙaramar Hukumar Dutsin-Ma, bisa wannan babban rashi.
Isma’il Adamu
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoBa Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
