Labarai
Ba Za a Amince da Raba Kafa a Zabukan 2027 Ba — Ministan Yada Labarai
Daga Aliyu Lawal, Minna
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya buƙaci mambobin jam’iyyar APC da su tabbatar sun zaɓi dukkan ’yan takarar jam’iyyar da ke neman muƙaman zaɓe a matakai daban-daban, daga sama har ƙasa, a babban zaɓen shekarar 2027, domin tabbatar da nasarar jam’iyyar.
Sai dai ya gargaɗe su kan raba kafa ta hanyar zaɓar ɗan takarar APC a wani mataki, sannan su zaɓi ɗan wata jam’iyyar siyasa a wani matakin. Ya ce hakan ba daidai ba ne, kuma jam’iyyar ba za ta amince da irin wannan hali ba.
Ministan, Mohammed Idris, wanda ya yi magana a madadin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin rantsar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamna na APC a Minna, babban birnin Jihar Neja.
Ya ce APC za ta yi nasara a babban zaɓen 2027 bisa la’akari da ayyukan da jam’iyyar ta gudanar domin samar wa ’yan Najeriya ribar dimokuraɗiyya, musamman a matakin ƙananan hukumomi da sauran al’ummomin ƙasa.
Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi kamfen ne bisa nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu cikin shekaru uku da rabi, waɗanda suka haɗa da bunƙasa ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, noma da kuma farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya, da sauran ayyukan da gwamnatin ta gudanar.
A cewar Idris Malagi, zaɓen Ambasada Ahmed Musa Ibeto da Gwamna Mohammed Umar Bago ya yi a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamna na APC ya dace kuma ya zo a kan lokaci, kasancewar yana daga cikin ’yan siyasar da suka fi ƙwarewa a muƙaman siyasa daban-daban.
Ya kuma buƙaci mambobin kwamitin da su gudanar da ayyukansu cikin himma da gaskiya domin cimma manufofin da aka tsara.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jihar za ta samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a zaɓen 2027.
Mohammed Umar Bago ya amince cewa Shugaba Tinubu yana ba su isassun kuɗaɗe, yana mai cewa yana son al’ummar Jihar Neja su zaɓi Tinubu domin jihar ta ci gaba da samun ƙarin kuɗaɗen da za su taimaka wajen kammala ayyukan raya ƙasa da ake gudanarwa.
Gwamnan ya kuma bayyana shirinsa na gudanar da bikin ƙaddamar da wani babban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamna na APC a Minna a mako mai zuwa. Ya ce ko dai shugaban ƙasa, mataimakinsa, shugaban Majalisar Dattawa, shugaban Majalisar Wakilai ko kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ne zai jagoranci ƙaddamarwar.
A jawabinsa, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa da Gwamna na APC, Ambasada Ahmed Musa Ibeto, ya gode wa Gwamna Bago bisa amincewar da ya nuna masa.
Sai dai ya yi alƙawarin ba zai yi wasa da wannan amana ba, yana mai jaddada cewa ƙarfin kowane kwamitin yaƙin neman zaɓe yana dogara ne da haɗin kai da aiki tare domin tabbatar da nasarar jam’iyya. Ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun cimma burinsu.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoRundunar ‘Yan Sanda Ta Tabbatar da Rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka
-
Labarai3 days agoSu Waye Suka Kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Tabbatar Da Nadin Kwamishinoni Shida
-
Kasuwanci3 days agoTsohon Ministan Harkokin Waje Gambari Ya Ƙalubalanci Matasa Kan Zaman Lafiya Da Gina Ƙasa
-
Kasuwanci3 days agoNijeriya Za Ta Fara Kera Makamai Da Kayayyakin Tsaro Masu Yawa
-
Labarai2 days agoMutane Aƙalla 64 Sun Mutu a Haɗarin Jiragen Ƙasa a Sifaniya
-
Labarai2 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Amince da Kudirin Kafa ’Yan Sandan Jiha
-
Labarai2 days agoKatsina: Dalibai 64 Sun Jikkata Bayan An Musu Rigakafin Cutar Tsargiya
