Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo da kuma sabunta cibiyar koyon sana’o’i da ke Kazaure.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Ya ce an amince da ware naira miliyan 690.8 domin gina sabuwar gonar kiwo ta zamani da kuma gyara wasu gine-gine a Cibiyar Inganta Kiwo da Samar da Ingantattun Dabbobi da ke Kazaure.
A cewarsa, aikin zai taimaka wajen inganta kiwo da yawan amfanin dabbobi, tare da bunƙasa wannan fanni cikin ɗorewa.
Ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙudurin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na ƙarfafa harkokin kiwo domin inganta wadatar abinci, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Kwamishinan ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da ware naira miliyan 432.87 domin gyara Cibiyar Koyon Sana’o’i da Horarwa da ke Kazaure.
Ya ce aikin zai inganta gine-gine da kayan aikin cibiyar domin samar da yanayi mai kyau na koyon sana’o’i da horar da matasa.
Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bai wa matasa ƙwarewar sana’o’in hannu, inganta damar samun aikin yi, ƙarfafa harkokin kasuwanci da dogaro da kai.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai5 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai6 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai6 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai6 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
-
Labarai3 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
