Labarai
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Nadin Sabbin Ministoci Biyu
Daga Bashir Meyere
Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin ministoci biyu da Shugaban Ƙasa ya miƙa sunayensu domin tantance su a matsayin ministoci.
Mutanen biyu su ne Joseph Tegbe daga Jihar Oyo da kuma Ambasada Sola Enikanolaiye daga Jihar Kogi, waɗanda aka tabbatar da su a matsayin ministoci a gwamnatin tarayya.
Hakan ya biyo bayan tantance su da aka a zaman majalisar, inda Sanatoci suka yi musu tambayoyi kan muhimman batutuwa da suka shafi bangaren wutar lantarki da harkokin ƙasashen waje, waɗanda su ne ma’aikatun da za su jagoranta.
Ana sa ran ministocin biyu za su cike gurbin da ya biyo bayan murabus ɗin wasu tsofaffin ministoci.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tunatar da Mista Joseph Tegbe cewa har yanzu aikin samar da wutar lantarki bai kai matsayin da ‘yan Najeriya ke bukata ba, tare da bukatar ya yi amfani da gogewarsa wajen sauya wannan yanayi.
Da suke amsa tambayoyin ‘yan majalisa, Mista Joseph Tegbe da Ambasada Sola Enikanolaiye sun jaddada cewa za su tabbatar da amincewar da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya nuna musu, tare da alkawarin yin aiki tare da Majalisar Dattawa domin sauke nauyin da ke kansu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
