Connect with us

Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Sabbin Nade-Nade Tare da Kafa Sabon Kwamitin Asibitin Yariman Bakura

Published

on

Daga Aminu Dalhatu 

Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin sabbin Mashawarta na Musamman guda biyu, da Babban Mataimaki na Musamman guda daya, da shugabannin wasu muhimman hukumomi, tare da sake kafa Kwamitin Gudanarwa na Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.

Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwad, ya ce nadin na da nufin karfafa gwamnati da inganta harkokin gudanarwa da hidimar jama’a.

Daga cikin nade-naden akwai Naziru Ibrahim a matsayin Mashawarci na Musamman kan Tsare-tsare da Gudanarwa, da kuma Nura Sani Abdullahi wanda ya koma Mashawarci kan Harkokin Siyasa.

Haka kuma, an nada Zainab Muhammad Hassan a matsayin Babbar Sakatariya ta ZAMCHEMA, yayin da Dr. Badamasi Sarkin Kaya Maradun zai jagoranci Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Tsafe. Namadi Isah Kasuwar Daji kuma ya zama Babban Mataimaki na Musamman kan Siyasa.

Gwamnan ya kuma sake kafa Kwamitin Gudanarwar Asibitin Yariman Bakura da ke Gusau, wanda Farfesa Lawal Suleiman Bilbis zai jagoranta, tare da sauran mambobi daga hukumomin lafiya da kungiyoyin kwararru.

Gwamna Lawal ya taya su murna tare da bukatar su gudanar da aiki bisa gaskiya da kwarewa don kawo cigaba a jihar.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara