Labarai
An Kafa Runduna Ta Musamman Don Dakile Manyan Laifuka a Kano
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kaddamar da wata runduna ta musamman mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU) domin karfafa yaki da manyan laifuka da inganta tsaro a jihar.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin ci gaba a kokarin rundunar na samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Bakori ya ce an kafa rundunar ne a ranar 24 ga watan Afrilun 2026, bisa umarnin shugabancin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya domin karfafa aikin leken asiri da inganta ayyukan tsaro.
A cewarsa, VCRU runduna ce ta musamman da aka kirkira domin magance matsalolin fashi da makami, garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran manyan laifuka a jihar.
Ya ce an tsara rundunar domin mayar da martani cikin gaggawa ga matsalolin tsaro, tare da dakile ayyukan masu aikata laifuka da tabbatar da bincike mai zurfi.
Kwamishinan ya ce jami’an rundunar an zabo su ne bayan tantancewa tare da ba su horo na musamman kan dabarun aiki, bayanan sirri da kare hakkin dan Adam.
Ya kara da cewa rundunar za ta dogara da bayanan sirri da hadin kan jama’a domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Haka kuma, rundunar ta kaddamar da Kwamitin Sa Ido na Fararen Hula domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kara amincewar jama’a ga ayyukan tsaro.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
