Ilimi
Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya
Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO.
Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Laraba.
Farfesa Wushishi ya ce Jami’ar Lead da Jami’ar Birmingham City da ke kasar Birtaniya sun tuntubi hukumar kan jarabawar da take shiryawa.
Ya Kara da cewar jami’o’in sun fara tunanin bai wa daliban Najeriya gurbin karatu da sakamakon jarabawarsu ta NECO.
A fahimtarsa, hakan na nuni da amincewa da ingancin sakamakon jarabawar NECO ne a idanun manyan jami’o’in ciki da wajen Najeriya.
Ya ce NECO ta cika sharudan Jami’ar Birmingham City, kuma a halin yanzu suna aiki tukuru kan ganin sun sami cika sharudan jami’ar Lead.
Aminiyya
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
