Ilimi
Birtaniya Ta Ware Fam Miliyan 19 Domin Karfafa Gina Makarantu da Cibiyoyin Lafiya A Kano
Gwamnatin Birtaniya, ta hannun ofishin kula da kasashen renon Ingila (FCDO) tare da haɗin gwiwar UNICEF, ta ware Fam Miliyan 19 domin ƙarfafa gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu jure sauyin yanayi a Najeriya.
A ƙarƙashin shirin samar da abubuwan dake jure yanayi na fari (CRIBS), Jihar Kano ta amfana da gyaran makarantu da asibitoci guda 55.
Wannan tallafi ya haɗa da sabunta makarantu 28 da cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 27, cikin haɗin gwiwa da gwamnatin Jihar Kano.

Yayin bikin ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara a ƙaramar hukumar Gezawa, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana cewa gyare-gyaren sun haɗa da hanyoyin zamani masu dacewa da sauyin yanayi, irin su ginin da ke da ƙarfin jure ambaliya, da kuma amfani da hasken rana don samar da wutar lantarki.
Ta kuma bayyana cewa gyaran zai ba mata damar haihuwa cikin aminci, tabbatar da samun magani cikin lokaci ga yara, da kuma bai wa matasa damar ci gaba da karatu ba tare da katsewa ba.
Daraktar ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja, Cynthia Rowe, wacce babbar mai ba da shawara kan ilimi na FCDO, Joseph Wales ya wakilta, ta bayyana cewa shirin CRIBS ya tabbata ne ta hanyar haɗin gwiwa da UNICEF, da Gwamnatin Tarayya, da Bankin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Sextant Foundation, JigSaw, Fab Inc, Crown Agents.

“Shirin CRIBS na nuni da yadda gine-ginen da ke jure sauyin yanayi za su iya inganta samun kulawa ga al’ummomi masu rauni. Muna fatan wannan tsari zai ƙara samun amfani a faɗin Najeriya,” in ji ta.
Haka kuma, UNICEF tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano, Gwamnatin Kanada, da IHS Towers Nigeria, sun ƙaddamar da na’urar samar da iskar numfashi ta oxygen a asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.
Tun da farko, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan ilimi Dr Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya bayyana wannan aikin a matsayin sauyi mai alfanu ga rayuwar al’umma.
Ya jaddada cewa ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara da kuma kaddamar da na’urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a jihar, sun zama ginshiƙi wajen samar da iskar da za ta ceci rayuka, musamman na yara da mata masu juna biyu.
Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar wajen karewa da kula da wadannan wurare domin cimma burin da aka sa gaba.
Abubuwan da suka fi jan hankali a taron sun haɗa da ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara, cibiyar kiwon lafiya ta Gofaro a Gezawa, kaddamar da na’urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a asibitin Muhammadu Buhari Specialist Hospital, Nassarawa LGA, da kuma ziyarar ban girma ga Gwamnatin Jihar Kano.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
